Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae, a karon farko da yayi magana dangane da fashewar tashar jiragen ruwa na Shahida Rajae ya gabatar da Ta’ziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikata a wannan hatsarin. Ya kuma bukaci a gudanar da bincike mai mai zurfi don gano musabbabin fashewar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jagoran yana bada umurni ga ma’aikatar shari’aa a kasar ta gudanar da cikekken bincike don sanin abinda ya faru saboda daukar matakan da suka dace don hana irin wannan sake faruwa nan gaba, sannan idan akwai wadanda suka yi kuskure a hukunta su.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gobarar da ta taso a tashar jiragen ruwa na Shahid Rajae, daya daga cikin tashoshin jirage masu muhimmanci a tattalin arzikin kasar, don haka dole ne a kara daukar matakan tsaro da amincin tashar don hana irin wannan sake faruwa.
Sanadiyyar wannan hatsarin majalisar dokokin kasar ta shelanta makoki a duk fadin kasar a yau Litinin. Sannan shugaban kasa Masoud Pezeshkiyan ya ziyarci tashar jiragen ruwa na Shahida Rajae don ganewa idanunsa abubuwan da suka faru da kuma barnan da aka tabka.
Ya zuwa yanzun wadanda suka rasa rayukansu sun kai 40 sannan wadanda suka rasa rayukansu sun kai dubu guda.