Jagora: Idan Amurka Ta Yi Barazana Ga Tsaron Iran Zata Fuskanci Mayar Da Martani

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Idan Amurka ta yi barazana ga tsaron kasar Iran, to lallai Iran ta kalubalance ta Jagoran juyin

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Idan Amurka ta yi barazana ga tsaron kasar Iran, to lallai Iran ta kalubalance ta

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Tattaunawa da Amurka ba wayo ba ce, kuma ba hikima ba ce, kuma gogewa ta tabbatar da hakan.

Yayin ganawarsa da tawagar kwamandojin sojojin sama da na sararin samaniya na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa: Idan Amurkawa suka yi barazana wa Iran, to lallai za su fuskanci mayar da martani, idan kuma suka aiwatar da wannan barazanar, to za su fuskanci mayar da martani Iran mai gauni, kamar yadda idan suka kawo hari kan kasar Iran, za su fuskanci mayar da martani kan harkokin da suka shafi tsaronsu ba tare da wata shakka ba.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kara da cewa: Zaman tattauna da gwamnati irin Amurka aiki ne na rashin hankali da rashin hankali da babu hikima ciki.

Jagoran ya kara da cewa: A cikin shekaru goma da suka gabata, Iran ta zauna kan teburin tattaunawa da Amurka, kuma aka kulla yarjejeniya a tsakaninsu, amma wanda ke jagorancin Amurka a yau, shi ne ya rusa wannan yarjejeniyar. Kuma a gabanin haka lamarin ya kasance, waɗanda mutane ba su mutunta duk wata yarjejeniyar da aka kulla da su, kuma manufar cimma yarjejeniyar ita ce dage takunkumi kan Iran, amma ba su dage shi ba!

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments