Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Hakuri da tsayin dakan mutane ne ya tilasta wa ‘yan sahayoniyya ja da baya
Shafin yada labarai na ofishin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei {r.a} ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na dandalin “X”, inda ya yi nuni da cewa: Tarihi ba zai manta da wadanda suka kashe dubban yara da mata a Gaza ba.
Jagoran ya kara da cewa: Za a rubuta a cikin littattafai cewa wata rana, wasu gungun mabarnata sun kashe dubban yara da mata a Gaza! Kuma kowa dai zai gane cewa hakurin al’ummar Falastinu da tsayin dakan ‘yan gwagwarmayar Falastinawa da jajircewar sauran bangarorin gwagwarmayar kasashe ne suka tilasta wa ‘yan sahayoniyya ja da baya daga mugun nufinsu na neman shafe wata al’umma daga kan doron kasa.