Jagora: Al’ummar Musulmi Zasu Iya Korar ‘Yan Sahayoniyya Daga Yankinsu

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Idan al’ummar musulmi suka yi amfani da karfinsu na cikin gida, to kuwa za su tumbuke yahudawan

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Idan al’ummar musulmi suka yi amfani da karfinsu na cikin gida, to kuwa za su tumbuke yahudawan sahayoniya daga yankinsu

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayin da yake karbar bakwancin, jami’an Iran, jakadun kasashen musulmi da kuma bakin taron hadin kan kasashen musulmi, ya jaddada cewa: Matukar al’ummar musulmi za su yi amfani da karfinsu na cikin gida, to kuwa zasu tumbuke yahudawan sahayoniyya daga yankin al’ummar musulmi kwata-kwata.

A daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi rahama Muhammad dan Abdullahi (s.a.w) da Imam Jafar al-Sadik (a.s), Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a safiyar yau Asabar ya tarbi tawagar jami’an kasar Iran, jakadun kasashen musulmi da kuma bakin mahalta taron hadin kan musulmi karo na 38 a Husainiyar Imam Khumaini (r.a).

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments