A Ivory Coast, Jam’iyyar (PPA-CI) ta bukaci tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo, ya yi mata takara a zaben shugabancin kasar na 2025.
An bayyana hakan ne a yayin taron kusoshin jam’iyyar a jiya Asabar wanda ya tattauna kan halin da kasar ke ciki.
Tuni Mista Gbagbo, wanda shi ne jagoran jam’iyyar ya amince da tsayawa takarar a zaben na 2025, kamar yadda sanarwar bayan taron ta ambato, amma sai a yayin babban taron jam’iyyar ne wanda ba’a tsaida ranar gudanar da shi ba za’a tsayar da Laurent Gbagbo din a hukumance a matsayin dan takarar jam’iyyar .
Sanarwar dai na zuwa ne a makonni biyu bayan da shugaban kasar Alassane Ouattara, ya yi wa wasu mutum 51 ciki har da tsaffin makusanta da kuma na hannun damanLaurent Gbagbo afuwa.
A watan Agustan da ya gabata dama tsohon shugaban kasar wanda kotun Hukunta manyan laifuka ta duniya ta wanke, ya bayyana cewa yana da sha’awar ci gaba da harkokin siyasa kuma mutuwa ce kawai za ta hana shi hakan.