Isra’ila Ta Yi Babban Kure, Na Kashe Haniyeh, Kuma Ba Makawa Iran Za Ta Mayar Da Martani_Pezehkian

Ministan harkokin wajen kasar Jordan, na wata ziyarar aiki a Tehran, a daidai lokacin da aka shiga zaman dar-dar a yankin biyo bayan kisan da

Ministan harkokin wajen kasar Jordan, na wata ziyarar aiki a Tehran, a daidai lokacin da aka shiga zaman dar-dar a yankin biyo bayan kisan da Isra’ila ta yi wa shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, Ismael Haniyeh, a birnin Tehran, wanda Iran ta sha alwashin mayar da mummunan martini.

Yayin ziyarar tasa, Ayman Safadi, ya gana da shugaban kasar Iran, Masoud Pezehkian, da ministan harkokin wajen kasar na riko, Ali Bagheri Kani, domin tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu dama yankin.

A ziyasar Safadi, ya isar da sakon sarki Abdullah na biyu ga shugaban kasar Iran kan halin da ake ciki a yankin da kuma alakar kasashen biyu.

Haka kuma, Safadi ya ce bai je da sako daga gwamnatin Isra’ila ba, kuma wannan ziyarar ta mayar da hankali ne kan alakar Iran da Jordan.

Ministan harkokin wajen kasar Jordan ya yi nuni da yadda kasarsa ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Haniyeh, tare da daukar wannan mataki a matsayin yunkurin Netanyahu na fadada yakin da ake yi a yankin.

Shugaban kasar Iran ya yi tir da kisan Isma’il Haniyeh da cewa “kuskure ne babba” da Isra’ila ta tafka, kuma ma makawa Iran za ta mayar da martini. 

Ziyarar da ba kasafai ba na ministan harkokin wajen na Jordan na zuwa ne kwana guda bayan da ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho da takwarorinsa na Iran da Masar game da kisan gillar da gwamnatin Isra’ila ta yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Tehran.

Jordan, wacce makwabciyar Isra’ila ce, wadda suke da yarjejeniyar zaman lafiya tun shekara ta 1994, babbar abokiyar hulda ce ta Amurka a yankin.

Ana dai ci gaba da nuna damuwa game da halin da ake ciki a yankin biyo bayan barazanar Iran da kawayenta na mayar da martani kan kisan na Ismael Haniyeh.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments