Isra’ila Ta Saki Fursunonin Falasdinawa Da Dama

Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa da dama a daidai lokacin da kungiyar Hamas ta mika gawarwakin ‘yan Isra’ila hudu ga kungiyar agaji ta Red Cross.

Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa da dama a daidai lokacin da kungiyar Hamas ta mika gawarwakin ‘yan Isra’ila hudu ga kungiyar agaji ta Red Cross.

Fursunonin sun isa birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan ne a kan motocin kungiyar agaji ta Red Cross bayan sun tashi daga gidan yarin Ofer da ke yankin da aka mamaye.

Musayar ta karkare kashi na farko na musayar da aka faro tsakanin bangarorin biyu, wanda ke gudana a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka fara aiwatarwa a watan da ya gabata da fatan kawo karshen yakin kisan kare dangi da gwamnatin Isra’ila ta yi wa Gaza na tsawon watanni 15.

Falasdinawan da aka sako na cikin fursunoni sama da 600, wadanda gwamnatin kasar ta ce za ta saki a matakin farko.

Baki daya, a matakin farko kungiyar Hamas ta mika ‘yan Isra’ila 33 da ta yi garkuwa dasu da suka hada da gawarwaki takwas, domin musayar fursunonin Falasdinawa kusan 2,000.

Tun ranar Asabar data gabata ce ya kamata gwamnatin Isra’ila ta mika fusunonin Falasdinawan su 206, saidai Isra’ila ta jinkirta sakin fursunonin bayan da kungiyar Hamas ta mika wasu ‘yan Isra’ila shida daga Gaza, tana mai cewa Hamas na wulakanta ‘yan kasarta a yayin bikin mika su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments