Isra’ila ta kashe Falasdinawa da dama tare da jikkata gommai a harin bam da dakarunta suka kai da sanyin safiyar ranar Lahadi a wani gida da ke yankin Tal al-Hawa na kudu maso yammacin Birnin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Falasdinawa, Wafa, ya ambato majiyoyi da dama a yankin suna cewa Isra’ila ta kashe mutane da yawa da jikkata gomma bayan ta rurga bama-bamai a gidan Abu Al-Auf da ke Tal al-Hawa, inda aka rika yi wa ma’aikatan agaji kiran gaggawa domin su kai dauki a gidan.
Tun daga ranar 7 ga watan Oktoban bara ne Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare a Gaza, inda ta yi wa ɗaukacin yankin ƙawanya.
Isra’ila ta kashe Falasdinawa fiye da 43,314, sannan an yi amannar cewa akwai dubban mutane da suka mutu a karkashin baraguzai, wadanda gine-gine suka danne su sakamakon rusa gidajensu da Isra’ila ta yi.