Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 3 A Wani Hari Da Ta Kai A Gaza

dakarun sojin isara'ila suka kai hari a gabar yammacin kogin jodan kuma yayi sanadiyar mutane mutane 3

Rahotanni daga yankin Gaza sun bayyana cewa wasu falasdinawa guda 3 sun mutu bayan da sojojin isra’ila suka kai hari a yankin, inda daya daga cikinsu matashi ne dan shekara 14 da haihuwa yayin da wasu guda 6 kuma suka jikkata a gabar yammacin kogin jodan

Hare haren baya bayan nan da sojojin Isra’ila suka kai a yau talata a wasu yankuna a gaza sun kashe matasa falasdinawa guda 2  da kuma wani mutum dan shekaru 43, yayin da wasu kuma suka jikkata wasu da dama kuma aka tilasta musu tserewa daga gidajensu.

Wani bafalasdine da yaronsa dan shekara 13 sun mutu bayan da jiragen isra’ila marasa matuki suk kai hari akan rufin gidansa a inda falasdinawa suka yi sansani a yankin zaitun dake kudu maso gabashin gaza, kuma matarsa da wani baflasdine kuma suka jikkata

Ma’aikatar lafiya ta yankin gaza ta bayyana cewa hare haren da isra’ila ta kai yayi sanadiyar mutuwar akalla falasdinawa 1615 tare kuma da  jikkata 5849 daga lokacin da aka kulla yarjejeniyar dakatar da bude wuta a ranar 10 ga watan oktoban shekara ta 2025

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted