Rahotanni sun bayyana cewa: sojojin HKI sun kaddamar da harin a Asibitin Al-shifa dake zirin gaza tare da bude wuta kan mai uwa da wabi da hakan yayi sanadiyar mutuwa da kuma jikkata Falasdinawa da dama.
Ministan lafiya a yankin Gaza ya bayyana cewa kimanin falasdinawa 30,000 ne suka rasa rayukansu da suka hada da fararen hula da marasa lafiya da suke jinya a Asibitin da kuma Ma’aikatan jinya ke da aiki a Asibirin
Gwamnatin Isra’ila ta yi Ikirarin rusa duk wani sansanin soji na kungiyar Hamas a yankin gaza sakamakon hare-haren ta kaddamar a makwanni da suka gabata a arewacin Gaza, don haka mayakan kungiyar sun boye ne a Asibitin na shifa kuma suke kai wa Isra’ila hari daga cikin Asibitin
Rahotan da gidan talabijin din Aljezeera ya fitar ya nuna cewa gine da ake amfanida shi wajen yin tiyata ga marasa lafiya ya kama da wuta, sakamakon lugudan wuta da sojojin Isra’ila suka yi,