Isra’ila ta harba makami mai linzami kan gidajen jama’a a birnin Damascus na kasar Syria

Ma’aikatar harkokin wajen Syria ta yi kakkausar suka dangane da harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kaddamar a kan gidajen jama’a  a birnin Damascus babban

Ma’aikatar harkokin wajen Syria ta yi kakkausar suka dangane da harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kaddamar a kan gidajen jama’a  a birnin Damascus babban birnin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 7 tare da jikkata wasu da dama.

A daren wannan Talata ce wasu makamai masu linzami na Isra’ila suka fada kan wani gini a unguwar Mezzah da ke yammacin birnin Damascus.

Kamfanin dillancin labaran SANA ya bayar da rahoton cewa, a bisa bayanan rundunar sojin Syria, akalla mutane 7 ne suka yi shahada da suka hada da mata da kananan yara, tare da jikkatar wasu 11 a wannan harin.

Majiyar ta kara da cewa ana ci gaba da aikin ceton wasu da suka makale a karkashin baraguzan ginin.

Ma’aikatar harkokin wajen Syria ta kira wannan hari na Haramtacciyar Kasar Isra’ila a matsayin wani mummunan laifi kan fararen hula da ba su ba su gani ba.

Syria dai ta sha yin kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki mataki kan wadannan hare-hare, wadanda take kallo a matsayin cin zarafi a fili da kuam keta huruminta a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Isra’ila ta sha kai hare-hare kan sansanonin soji a cikin kasar Siriya, musamman na kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa sojojin Siriya a yakin da suke yi da ‘yan ta’adda da ke samun goyon bayan kasashen ketare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments