Gwamnatin Isra’ila ta tura wa tawaga zuwa kasar Qatar a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin Isra’ilar da masu shiga tsakani ciki har da Amurka.
Wannan ya biyo bayan tattaunawar kai tsaye da ba a taba yin irinta ba tsakanin Hamas da wakilin Amurka Adam Boehler dake kula da mutanen da akayi garkuwa da su.
Wakilin na Amurka ya sha bayyanawa a baya baya nan cewa Ya yi imanin cewa za a iya cimma yarjejeniya a makonni masu zuwa.
Ya kuma ce Hamas ta shirya tsagaita bude wuta na tsawon shekaru biyar zuwa goma sannan kuma kungiyar ta kwance damara.
Tunda farko dai kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, “suna kira ga masu shiga tsakani a Masar da Qatar, da kuma gwamnatin Amurka, da su tabbatar da cewa ‘yan mamaya sun mutunta yarjejeniyar, da ba da damar shigar da kayayyakin jin kai, da kuma ci gaba da tafiya mataki na biyu na tsagaita.
A nata bangaren dai Isra’ila na son tsawaita wa’adin zangon farko na tsagaita bude wuta har zuwa tsakiyar watan Afrilu, kuma ta bukaci ficewar Hamas daga yankin Falasdinu da ta ke mulki tun shekara ta 2007, da kuma dawo da ragowar mutanen da taka garkuwa da su.