Isra’ila Da Taiwan Barazana Ne Ga Somaliya_Sheikh Mohamud

Hassan Sheikh Mohamud ya bayyana cewa Taiwan na barazana ga wanzuwar Somaliya.

Shugaban Somaliya ya yi gargadin cewa Isra’ila da Taiwan barazana ce ga hurumin kasarsa da kuma ikon mallakar yankunanta bayan da Isra’ila ta amince da yankin Somaliland da ya balle, da kuma karfafa dangantaka tsakanin Taiwan da Isra’ila.

Hassan Sheikh Mohamud ya bayyana cewa Taiwan na barazana ga wanzuwar Somaliya, yayin da Isra’ila ke barazana ga matsayinta na kasa.

Shugaban Somaliya yana magana ne a ranar Lahadi, a wani bikin tunawa da gina Jami’ar Tsaron Kasa ta Somaliya a babban birnin kasar.

Ana kuma sa ran aikin, wanda China ta dauki nauyinsa, zai kunshi asibiti ga sojojin Somaliya.

Shugaban Somaliya ya sake jaddada alaka ta kud da kud tsakanin Somaliya da Beijing, yana mai bayyana China a matsayin daya daga cikin kawayen kasar na kud da kud.

Somaliland ta ayyana ‘yancin kanta daga Somaliya a shekarar 1991, amma ba ta samu karbuwa daga kasashen duniya ba.

A watan Disamba na shekarar 2025, Isra’ila ta zama kasa ta farko da ta amince da yankin da ya balle.

A watan Yunin 2026, wani babban jami’in gwamnatin Somaliya ya Ambato cewa, Isra’ila ta tura gungun mutane 50 zuwa Somaliland jim kadan bayan ta amince da yankin.

Gwamnatin tarayya ta Somaliya ta yi watsi da wannan amincewa da aka yi mata, tana mai cewa haramun ne kuma ta sake nanata cewa Somaliland muhimmin bangare ne na kasar mai ‘yancin kai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted