Irawani: Goyon  Baya Maras Iyaka Da Amurka Take  Bai Wa “Isra’ila” Ya  Kara Mata Wauta

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’id Irawani ya bayyana cewa; Yadda Amurka take daure wa ‘ Isra’ila’ gindi yana sa tana kara wauta.

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’id Irawani ya bayyana cewa; Yadda Amurka take daure wa ‘ Isra’ila’ gindi yana sa tana kara wauta.

Jakadan na jamhuriyar musulunci ta Iran wanda ya gabatar da jawabi a jiya Litinin da dare a yayin zaman musamman da kwamitin tsaro ya yi dangane da harin da HKI ta kawo wa Iran, ya cigaba da cewa, goyon baya maras haddi da Amurkan take bai wa HKI ya sa wautarta  tana  karuwa, don haka  take cigaba da kai hare-hare a cikin Gaza, Lebanon yanzu kuma a Iran da hakan yake raunan zaman lafiya a cikin wannan yankin.

Sa’id Irawani ya fara jawabinsa da yin godiya ga kwamitin tsaro da ya amsa kiran na Iran na yin wannan taro, domin tattauna harin da HKI ta kawo wa Iran, ya kuma yi godiya ta musamman ga kasashen Aljeriya,  China da kuma Rasha wadanda su ka nuna goyon bayansu na yin wannan taron.

Bugu da kari jakadan na Iran ya yi godiya ga dukkanin kasashen da su ka yi tir da Allawadai da harin na ‘yan sahayoniya akan Iran.

Sa’id Irawani ya kuma ambato wasikar da ministan harkokin wajen Iran ya rubuta wa babban sakataren MDD da a ciki ya bayyana harin na ‘yan sahayoniya na ganganci da cewa keta dokokin kasa da kasa ne da kuma dokokin MDD.

Jakadan na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kuma ce; Martanin da Iran din za ta mayar zai kasance ya dace da dokar majalisar  Dinkin Duniya mai lamba ta 51 da kuma dokokin kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments