Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin ruwa na rudunar kare juyin musulunci na iran sun ce wasu jiragen mai guda biyu sun kama da wuta bayan da suka yi kunnen uwar shegu da gargadin da ake yi musu suka yi kokarin satar hanya da ya kai ga sun ci karo da nakiyoyin da aka dasa, lamari da ya jawo suka kama da wuta inda hayaki ya turnuke a kusa mashigar Hormuz
A cikin wani bayani da ofishin kula da hulda da jama’a na dakarun IRGC ya fitar yau talata yace daya daga cikin jiragen mai ya kama da wuta bayan da yaci karo da nakiyoyin da aka dana, yayin da tanka ta biyu kuma dake aiki karkashin kariyar jiragen saman yaki na Amurka ya hadu da hadari kuma ya kama da wuta a lokacin da yake kokarin wucewa ta mashigar a boye ta barauniyar hanya
Tuni dai dakarun sojin ruwa na kasar iran suka yi gargadin cewa babu tsaro a hanyoyin da ta hana abi, kuma duk jiragen ruwan da suke aiki da dakarun Amurka za su fuskanci irin wannan sakamakon idan suka yi kokarin karya doka.
kwamadan dakarun kare juyin na kasar iran ya jaddada cewa alkawarin karya da amurka ta yi na yin rakiya da kuma bada kariya suna kara tabbatar da karyarta mara tushe inda jiragen ruwan da suka yarda da ita suke konewa ko kuma suke fuskantar wulakanci