Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun tabbatar da shahadar Majo Janar Abbas Nilfrushan a hare haren da jiragen yakin HKI suka kai a kan birnin Beiret a ranar jumman da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar dakarun na fadar haka a yau Asabar. Ta kuma kara da cewa, Janar Nilfrushan yana daga cikin sojojin kasar Iran masu bada shawara ga dakarun kungiyar Hizbullah a kasar ta Lebanon.
Kafin haka dai Janar Nilfrushan ya na daga cikin wadanda suka yi yakin shekaru 8 da gwamnatin kasar Iraki a farko farkon kafa JMI Sannan ya rike mukamai da dama a ciki rundunar, ya taba zama mataimakin kwamandan sojojin kasa na rundunar IRGC, sannan ya rike shugabancin makarantar horar da sojojin JMI.
Banda haka “Brigadier General Nilfrushan ya taimaka a ayyukan tsaron wurare masu tsarki a kasashen waJe da kuma ayyuka da dama na kwace masallacin alaksa a kasar Falasdinu da aka mamaye.
Daga karshen yana aiki a matsayin mai bada shawara ga kungiyar Hizbullah a dabarbarun yaki, har zuwa ranar jumma’an da ta gabata a lokacinda yayi shahada tare da shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah.