Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta bayyana hannun hukumomin leƙen asiri guda 10 na ƙasashen waje a cikin tarzomar da ta faru kwanan can a Iran
Shugaban bangaren leƙen asiri na rundunar kare juyin juya halin Musulunci, Birgediya Janar Majid Khademi, ya sanar da cewa: Aƙalla hukumomin leƙen asiri na ƙasashen waje 10 ne suka shiga cikin abubuwan da suka faru a watan Janairun da ya gabata, yana mai bayyana waɗannan abubuwan a matsayin yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba wanda al’ummar Iran suka murƙushe.
Birgediya Janar Khademi ya tabbatar da cewa: Hukumomin leƙen asiri na ƙasashen waje ne suka gudanar da tsare-tsare, daidaitawa, da kuma kula da hanyoyin sadarwa na filin, musamman yana mai nuni da rawar da rundunar leƙen asiri ta 8200 ta Isra’ila ke takawa, wacce ke gudanar da asusu da miliyoyin na’urorin kwamfuta a shafukan sada zumunta.
Ya bayyana cewa: Jami’an tsaro sun kira mutane 2,735 da ke da alaƙa da ƙungiyoyin masu adawa da Iran, sun yi gargaɗi ga kimanin mutane 13,000 kan muggan dabi’unsu, sun kuma kama makamai 1,173 marasa lasisi da aka shigo da su cikin kasar, sannan suka gano tare da kama mutanen da ke da alaƙa da hukumomin leken asirin ƙasashen waje.