IRGC: Iran ba za ta fara yaki ba amma za ta mayar da martani ga duk wata barazana

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi gargadin cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba neman wata kasa

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi gargadin cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba neman wata kasa da yaki ba, amma kuma  a lokaci guda ta shirya tsaf domin mayar da mummunan martani ga duk wata barazana ko shishigi daga makiya.

Janar Hossein Salami ya bayyana hakan ne a wannan Lahadi, bayan da Washington ta zargi Tehran da taimakawa sojojin Yaman a hare-haren da suka rika kaiwa haramtacciyar kasar Isra’ila a baya-bayan nan tare da yin kira da ta daina yin wanann zargi maras tushe balantana makama.

Salami ya ce, “Iran ba za ta taba zama mai fara yaki ba, amma idan aka fuskanci barazana, za ta mayar da martani mai tsanani.”

Shugaban kasar Amurka ya sake alakanta ayyukan da kungiyar Ansarullah ta Yaman ga Iran, ya kuma ce dole ne Iran ta daina  goyon bayan kungiyar mai gwagwarmaya.”

Salami ya jaddada cewa, mutanen Yemen al’umma ce mai ‘yanci da ke bin manufofi na kashin kansu ba tare da an yi musu katsalandan ba. In ji babban kwamandan na IRGC.

Salami ya jaddada cewa, “Mu ba al’ummar da ke gudanar da ayyukanta cikin sirri ba ne; a maimakon haka, muna yin komai a bisa doka da oda da kuma kiyaye ka’idoji na duniya, kuma komai namua  fili yake, kuma lokacin da muka dauki matakin soji a kan Isra’ila ba mu boye ma kowa ba kamar yadda duniya ta sheda hakan a cewar janar Salami.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments