IRGC : Duk wani hari ba zai takaita ga iyakokin Iran ba

Ikirarin na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka da Isra'ila ke ci gaba da barazanar daukar matakin soji kan Iran.

Rundinar kare juyin juya musulinci ta Iran, ta bayyana cewa duk wani hari kan kasar ba zai takaita kan iyakokin Iran ba.

Kakakin rundunar ta (IRGC) ya bayyana cewa rikicin da ake yi da Amurka da Isra’ila a yanzu zai iya haifar da illa ba wai ga Iran ba kawai zai iya shafar makomar sauran kasashe a yankin.

Birgediya Janar Hossein Mohebbi ya tabbatar a ranar Asabar, cewa rikicin da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Amurka, da Isra’ila ya wuce na soji, makiyan na yaki ne da al’adu, addini, da wayewar Iran.

Ya jaddada cewa Dole ne al’ummar Iran su fahimci yanayin rikicin da ake ciki a yanzu, su kiyaye hadin kan kasa, sannan su dogara da karfin kasarsu don tantance makomarta in ji shi.

Ikirarin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka da Isra’ila ke ci gaba da barazanar dokar matakin soji kan Iran.

Shugaba Trump, ya bayyana a baya baya nan cewa ko dai iran ta cimma yarjejeniya ko ta fuskanci hari a wannan Lahadin.

Kasashen duniya da dama ciki har da na yankin na ci gaba da gargadin cewa a fifita hanyoyin diflomatisya maimaikon amfani da karfin soji.

Ministan harkokin wajen Turkiyya ya yi gargadin cewa wani sabon hari kan Iran zai kara yaɗa yaƙi da rikici a yankin yayin da tashin hankali tsakanin Washington da Tehran ke ƙara ta’azzara.

“Shiga tsakani na soja a Iran ba mafita ba ce ko kaɗan. Babu wanda ke goyon bayan wannan a yanzu,” kamar Hakan Fidan ya shaida wa manema labarai a ranar Juma’a bayan taron R4+E3 a Istanbul, taron farko da aka taɓa yi a wannan tsari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted