Iran: Zahra Kiyani Ta Lashe Lambar Zinari A Gasar Wushu A Karon Farko

Zahra Kiana yar wasan Wushu ta lashe lambar Zinari a wasar Wushu ta shekara ta 2025 a kasar Barazil. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar

Zahra Kiana yar wasan Wushu ta lashe lambar Zinari a wasar Wushu ta shekara ta 2025 a kasar Barazil.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa Kiyani ta lashe lambar Zinari ne a dai-dai lokacinda wannan wasan take sabo a kasar Iran, kuma tana cike da masu taka rawa a cikinta da dama daga gabacin kasashen Asia.

Labarin ya kara da cewa Kiyani ta daukaka kasar Iran a gasar Wushu, sannan ta kwadaitar da sauran mata wadanda suke sha’awar yi wasar.

A rana ta 4 da fara gasar Wushu ta kasa da kasa kuma karo na 17th ta shekara ta 2025 a kasar Brazil Kina ta lashe lambar Zinari, wanda ya bawa Iran matsayi a wannan wasan a duniya a cikin yan wasa 27 da suka shiga gasar.

Kiyani ta sami maki 9.763 wanda shi ne ya bata zama zakara da lambar zinari a gasar.

A lissafin irin wannan wasar

Zahra Kiani (Iran): 9.763, Indonesia: 9.756, Vietnam: 9.746.

An fara gasar a ranar Asabar 6 ga watan Satumba, tare da halattar dukkan yan wasa 27 daga kasashen duniya ta zami wannan nasarar, a karon farko wa kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted