Shugaban majalisar shawarar musulunci na kasar Iran mohammad Baqeer Qalibaf ya bayyana cewa iran ashirye take domin tunkarar duk wani wuce gona da iri akan kasarta, wajen mayar da martani da ba’a yi tsammani ba kan makiya, yace babu wanda zai yi wa kasar barazana da yaki ko kisa
Da yake bayani a zaman majalisar da aka gudanar a yau , shugaban ya kara da cewa babu wanda zai yi mana barazana, kuma a shirye muke mu mayar da martani kan duk wani harin ba zata da makiya za su kawo kan kasar iran
Qalibaf yace kasar Amurka ta jefa kanta cikin wani mawuyancin hali sakamakon kuskuren lissafin da ta ya, da kuma yaki da ta kaddamar kan kasar Iran ba tare da wani dalili ba, don haka ya ragewa amurka ta dauki mataken da suka dace domin kubutar da kanta daga wannan mawuyacin yanayi.
Daga karshe yace yanzu Amurka ta kasa fahimtar babbancin dake tsakanin iran ta yau da kuma kasar a lokacin tsohon tsarin mulkin sarauta wanda Washington ke goyon baya, inda kasashen wajen suka kasance suna da tasiri sosai kan harkokin kasar