Iran: Yawan Kayakin Da Ake Saya Daga Iran Zuwa Iraki Ya Kara Yawa

Kayakin da ake saya daga kasar Iran zuwa kasar Iraki ya karu da kashi 27 % idan an kwatanta da shekarar da ta gabata. Kamfanin

Kayakin da ake saya daga kasar Iran zuwa kasar Iraki ya karu da kashi 27 % idan an kwatanta da shekarar da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran IRIB.NEWS ya bayyana cewa a cikin watanni uku da suka gabata na wannan sabuwar shekarar Iraniyawa, wato shekara ta 1403 ya kara da kimani dalar Amurka biliyon 3.

Labarin ya  kara da cewa mai bawa shugaban hukumar bunkasa kasuwanci na JMI da kuma jami’I mai kula da harkokin kasuwanci na kasar Iran a kasar Iraki sun bayyana cewa yawan kayakin da aka saya daga kasar Iran zuwa Iraki ya karu da kashi 27%. Sannan kimarsa ya karu daga dalar Amurka biliyon 2,346 a dai dai wannan lokacin a shekarar da ta gabata, zuwa dalar Amurka biliyon 3,650 a wannan shekara.

Labarin ya kara da cewa nau’in kayakin da aka fi sayansu a cikin wannan lokacin sun hada da iskar gas na dafa abinci, karafunin gine gine ko rodi, tuffah, da sauransu.

Labarin ya kara da cewa an sami kayaki da aka shigo da su kasar Iran daga Iraki wadanda suka kai dalar Amurka miliyon 107.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments