Iran ta bakin ministan harkokin wajen kasar ta bayyana cewa bata son yaki amma kuma a shirye ta ke ta kare hurimin kasarta.
”Muna shirye idan yaki ne, haka ma a shirye mu ke idan zaman lafiya ake so” Inji Ministan harkokin wajen aksar ta Iran Seyyed Abass Araghchi.
Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a binrin Bagadaza bayan ganawarsa da ministan harkokin wajen Iraki.
A nasa bangare ministan harkokin wajen Iraki, Fouad Hussein, ya bayyana cewa Iraki ba zata lamunta a yi amfani da sararin samaniyarta ba wajen kai hari kan Iran.
Araghchi Ya isa babban birnin kasar Iraki ne a wani bangare na rangadin da ya kai a kasashen Lebanon, Siriya da Saudiyya a kokarin samar da zaman lafiya mai adalci a Gaza da Lebanon.”