Iran : Ya Zama Wajibi A Yi Amfani Da Duk Karfin Da Ake Da, Wajen Takawa Isra’ila Birki A Gaza

Ministan harkokin wajen rikon kwarya na kasar Iran, Ali Bagheri Kani, ya ce, ya zama wajibi a  yi amfani da duk karfin da ake da

Ministan harkokin wajen rikon kwarya na kasar Iran, Ali Bagheri Kani, ya ce, ya zama wajibi a  yi amfani da duk karfin da ake da shi wajen takawa gwamnatin Sahayoniya birki a kisan kiyashin da take ci gaba da aikatawa a zirin Gaza.

Mista Kani, ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, Ismael Haniyeh a binrin Doha na kasar Qatar.

Bai kamata a tsaya a rufe ido kan laifuffukan da ake yi wa al’ummar Gaza ba, kamata ya yi a tsayin daka kan tsayin daka a kan ‘yan mamaya ba.”

Ya kara da cewa, bai kamata a ce gwagwarmayar da ‘yan mamaya na Isra’ila ta kasance da makami kadai ba, tilas ne a dauki matakai na shari’a, tsayin daka na siyasa, da tsayin daka a fagen diflomasiyya domin kare hakkokin Falasdinawa.

A nasa bangaren, shugaban ofishin siyasa na Hamas, Haniyeh ya nuna jin dadinsa ga Iran bisa goyon bayan da take baiwa al’ummar Falasdinu.

Ya kuma bada misali da irin zanga-zangar kin jinin Isra’ila a kasashen Yamma da Amurka, da kuma jajircewar ‘yan gwagwarmaya a Lebanon da Yemen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments