Iran : Wadanda Suka Dage Kan Tattaunawa Da Iran, Na Yi Ne Don Amfanin Kansu_ Jagora

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce dagewar da wasu kasashe masu cin zarafi suka yi na yin shawarwari

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce dagewar da wasu kasashe masu cin zarafi suka yi na yin shawarwari da Iran na yi ne don neman amfanin kansu.

Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da manyan jami’ai na bangarori uku na gwamnati a ranar Asabar.

Jagoran ya ce “Dagewar da wasu gwamnatoci suka yi kan yin shawarwari ba wai don warware al’amura ba ne, a’a yana nufin aiwatar da abin da suke so.”

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: ” Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta amince da abin da suke tsammani ba.”

Wadannan gwamnatocin da suke cin zalin ba sa neman yin shawarwari kan batun nukiliya kawai; A maimakon haka, suna amfani da shawarwari a matsayin “hanyar cimma manufofinsu” a fannoni kamar karfin tsaron Iran da karfin kasa da kasa, wadan ko shakka babu Iran za ta yi watsi dasu.

Ya kara da cewa, suna tabo batun tattaunawar ne domin matsa lamba kan ra’ayin jama’a, don haka Iran ta ki yin shawarwari da su, duk da cewa sun nuna a shirye su ke.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments