Iran Tasha Alwashin Ruguza Muhimman Cibiyoyin ‘Yan Sahayoniyya A Hari Na Gaba

Mai ba da shawara ga kwamandan kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Za su ruguza cibiyoyin Isra’ila idan har ta sake

Mai ba da shawara ga kwamandan kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Za su ruguza cibiyoyin Isra’ila idan har ta sake kai hari kan kasar Iran

Mai ba da shawara ga kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ibrahim Jabbari ya yi watsi da da’awar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta shirin kaddamar da yakin kan Iran a matsayin martani ga harin daukan fansa da Iran ta kai kanta na farmakin “Alkawarin Gaskiya”.

Birgediya Janar Jabbari ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da tashar Al-Alam ta kasar Iran, inda ya bayyana cewa: ‘Yan sahayoniyya  ba wai ba sa son kai hari kan Iran ba ne, amma ba sa da karfin gwiwar kaddamar da hari kan Iran ne saboda tsoron abin da zai biyo baya.

Janar Jabbari ya jaddada ewa: Bangaren gwagwarmaya yana da fadi, kwarewa, jajurcewa da kuma babban hadin kai wajen kalubalantar duk wanda ya dauki matakin wuce gona da iri kansa.

Ya kara da cewa: Kasar Yemen tana da ‘yan gwagwarmaya da sukahaura miliyan daya da suke shirye don yin jihadi, kuma akwai da yawa irinsu a kasashen musulmi da dama.

Ya kuma bayyana cewa a shirye suke su kalubalanci duk wata arangama, kuma sun fara nuna wasu daga cikin karfinsu, kuma akwai karfin da ba su bayyana ba tukuna, kuma za su bayyana su a lokacin da ya dace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments