Iran Tana Iya Yayyanke Kabulolin Internet A Hurmuz

Yakin da Amurka da HKI suka dorawa Iran ya yi sanadiyyar jawo matsalolin tattalin arziki ga duniya gaba daya daga ci har da Amurka da

Yakin da Amurka da HKI suka dorawa Iran ya yi sanadiyyar jawo matsalolin tattalin arziki ga duniya gaba daya daga ci har da Amurka da kuma kasashen Turai, saboda rufe mashigar ruwa ta Hurmuz wanda Iran ta yi. Kafin yakin dai wannan mashigar a bude take, kuma kowa na wucewa.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto sakataren majalisar koli ta harkokin tsaron kasar Iran Janar Muhsen Rezaie yana fadar haka, a wata hira ta musamman da tsahar.

Ya kuma kara da cewa, banda mashigar ruwa ta Hurmus JMI tana da wani zabi idan an kaita bongo tana iya fakewa da shi, wanda kuma shi ne yanke manya manyan wayoyin hasken internet wadanda suka ratsa da mashigar ruwa ta Hurmuz har guda 7.

Rezaei ya kara da cewa, akwai wasu manya manyan wayayin hasken Internet masu muhimmanci wadanda suka ratsa ta mashigar ruwa ta Hurmuz, wadanda mutane iya katsesu.

Ya ce wayoyin sun hada da FALCON mai tsawon kilomita 10,300 km, wanda kuma yak e zuwa kasar India, da Sri Lanka da kuma kasashen yankin Tekun Farisa. Sai kuma Gulf Bridge Intl. wanda yake da tsawon kilomita 5,270 wanda ya hada kasuwannin kasashen tekun farisa da internet sannan akwai MENA mai tsawon kilomita 8,000 wanda ya hade kasar Omman da Saudia da Masar da kuma Italia, har ila yau da kasashen tekn Medeteraninan da Internet.

Ya ce idan an sake kaiwa Iran hare hare suna iya lalata wadanda wayayi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted