Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa tattaunawa tare da barazana ba tattaunawa ake kiransa ba, sai dai tursasawa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmael Baghaie ya na fadar haka a yau litinin a jawabin mako-makon da ya saba gabatarwa a ko wace ranar litinin.
Baghaei ya kara da cewa JMI ba zata taba tattaunawa da Amurka tare da barazana da kuma takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki ba. Zabin tattaunawa ko kuma yaki, ba tattaunawa sai dai tursasawa.
Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa JMI ba ta da zabi, ko ta shiga tattaunawa da Ita Amurka ko kuma ta shiyawa yaki. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ya kara da cewa takunkuman tattalin arziki mafi muni wanda Amurka ta dorawa kasar tun shekara ta 2018, sun yi illa da kuma tasiri kan rayuwar mutanen kasar Iran, amma wannan bai sa ta mika kai ga bukatun Amurka ba. Ya kuma kara da cewa ko yakin ma, ba zai tilsatawa kasar Iran mika kai ga bukatunta ba.
Abinda Trump yake kira tattaunawa shi ne wakilan kasar Iran su zauna kan wani teburi, sannan Amurka ta ce, ga abinda zaki yi, ga abinda zaki bari, idan kunki yin haka, to ga makamai.
Ya ce, tattaunawa kam, Iran ta yi hakan a yarjeniyar JCPOA kuma an dauki shekaru biyu cur ina tattaunawa tsakanin kasashe 5 +1 da Iran, daga ciki har da ita Amurka.