Kungiyar ‘yan wasan ” Taekwondo” Iran dake kasa a shekaru 21 sun zama gwarazan duniya da aka yi a birnin Nairobi na kasar Kenya, bayan da su ka sami zinariya 3 da azurfa 1 sai kuma tagulla biyu.
Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto cewa; a jiya Asabar ne aka kawo karshe gasar wasan na ” Taekwondo” wanda ya sami halartar ‘yan wasa 452 daga kasashe 75.
A ranar ta karshe ta wasan, dan wasan Iran Muhammad Aizadeh, ya sami azurfa, sai kuma wani dan wasan “Matin Rizayi wanda ya sami tagulla.
Wadanda su ka sami zinariya kuwa su ne Abul Fadl Zandi, da Radin Zinalu sai kuma Amir Riza Gulami.
Kasar Turkiya ta zo ta biyu da ta sami zinariya biyu da azurfa daya, sai kasar Khazakistan wacce ta zo ta uku da ta sami zinariya biyu da tagulla daya. Kasar da ta biyo bayanta ita ce Masar da da Bulgaria sai India.
A fagen mata kuwa, Iraniyawa 6 ne su ka sami kyautuka, inda kungiyarsu ta zo ta hudu.
An kuma zabi Majid Afkali na Iran a matsayin mai bayar da horo na daya, sai kuma Abul Fadl Zandi wanda aka zaba a matsayin dan wasa na farko.