A yau Laraba ne aka sanar da zaman Iran memba a cikin wannan kungiyar ta ( ISKO) wacce aka bude reshenta a cikin kasa tun a 2011.
Farfesa Rahmatullah Fattahi ne ya bude reshen kungiyar ta ” Ilimomin Tattara Bayanai Da Kere-Kere” wacce kuma ta ci gaba da gudanar da ayyukanta har zuwa 2019. An sami tsaiko a yadda kungiyar take tafiyar da ayyukan nata, saboda bullar Korona, amma ta ci gaba da aiki a karkashin wani tsari na musamman ( IranDoc.). Aikin wannan cibiyar shi ne tsara gudanar da nazarori da bincike na ilimomi mabanbanta da kuma hana yin maimaici akansa.
A halin yanzu da akwai mutane 20 da suke aiki a karkashin wannan kungiyar daga asalin su 20 da aka fara bude reshenta da su. Wadannan mambobin na yanzu suna kuma aiki ne da cibiyar “IranDoc” wacce shafinta na internet ya koma karkashin waccan cibiyar.
A cikin watan Nuwamba na 2026 ne ake sa ran gudanar da taron karawa juna sani akan kungiyar a Iran. Haka nan kuma abu ne mai yiyuwa duk bayan shekaru biyu, kungiyar ta rika yin taron kasa da kasa