Iran Ta Yi Watsi Da Rahotannin Kitsa Kai Hari Washington

Mista Araghchi ya bayyana cewa Babu gaskiya sam a wannan labarin.

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta yi watsi da rahotannin da wasu kafofin yada labarai na Amurka suka rawaito cewa, Tehran na shirin kai hari Washigton.

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi watsi da rahotannin da kafafen yada labarai na ciki har da CNN da New York Times, suka rawaito yana mai cewa “ba gaskiya ba ne.

Ya bayyana cewa wadannan zarge-zargen wani bangare ne na ”yakin karya” kan Jamhuriyar Musulunci.

“A cikin awanni 72 da suka gabata, kafafen yada labarai masu goyon bayan Isra’ila sun rawaito cewa Iran na shirin amfani da makamai masu guba a Washington, yayin da a lokaci guda take gina sansanonin makamai masu linzami a karkashin madatsun ruwa.

Mista Araghchi ya bayyana cewa Babu gaskiya sam a wannan labarin.

Ita ma tawagar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta yi watsi da labarin da jaridar New York Times da kuma CNN kan Iran.

Ta bayyana wadannan rahotannin a matsayin labaran karya da aka kirkiresu don samar da hujjar ci gaba da kai hari kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, in ji tawagar a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.

Iran ta sake tinatar cewa kai hari kan muhimman kayayyakin more rayuwa na farar hula laifi ne na yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted