Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Tsibiran guda uku na Tunb Babba da Tunb Karami da Abu Musa yankuna ne Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da ikirari da kungiyar hadin kan kasashen Larabawan yankin tekun Fasha (PGCC) ta yi dangane da tsibiran Iran guda uku, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da tsaro da muradun kasar a cikin tsibiran guda uku.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya jaddada matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da yin watsi da ikirarin da ke kunshe a cikin bayanin karshe na taron ministocin harkokin wajen kasashen yankin tekun Fasha karo na 64 dangane da tsibiran kasar Iran guda uku na Tunb Babba, Tunb Karami da Abu Musa.
Baqa’i ya yi watsi da zarge-zargen da ke kunshe cikin wannan bayani dangane da hukunci da matakan shari’a da hukumomin Iran da abin ya shafa suka dauka dangane da tsibiran da aka ambata, yana mai cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta dauki duk wani matakin da ya dace don tabbatar da tsaro da muradun kasar a cikin tsibiran guda uku, da suka hada da filayenta, ruwa, da sararin samaniyarta, daidai da hakkinta na ‘yancin kai.