Search
Close this search box.

Iran ta yi watsi da batun cewa tana yin kutse a cikin lamarin zaben Amurka

Wakilin dindindin na Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya yi watsi da zarge-zargen da gwamnatin Amuka ta yi kan cewa Iran din tana yin kutse

Wakilin dindindin na Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya yi watsi da zarge-zargen da gwamnatin Amuka ta yi kan cewa Iran din tana yin kutse a cikin lamarin zaben shugaban kasar Amurka na 2024, yana mai cewa hakan zargi wanda babu hujja a kansa.

Kafofin yada labaran Amurka sun tambayi tawagar jami’an diflomasiyyar Iran kan martanin da zasu mayar  ga wannan sanarwa da hukumomin leken asiri na gwamnatin Amurka suka fitar a ranar Litinin, inda suka zargi Tehran da yunkurin yin katsalandan a zaben shugaban kasa na 2024 da kuma kai hari kan kamfen siyasa da jama’ar Amurka da ayyukan ta’addanci da kuma hankoron yin tasiri a zaben.

“Irin wadannan zarge-zargen ba su da wata hujja. Kamar yadda muka sanar a baya, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta da niyyar yin katsalandan a zaben shugaban kasar Amurka,” a cewar tawagar Iran a cikin wata sanarwa.

Ya kara da cewa, “Idan gwamnatin Amurka da gaske ta yi imani da ingancin ikirarinta, ya kamata ta ba mu hujjojin da suka dace – idan akwai – wanda za mu mayar da martani ga hakan.”

A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, Ofishin Bincike na Tarayya a Amurka (FBI), ofishin daraktan hukumar leken asiri ta kasa da tsaro na hanyoyin yanar gizo, da hukumar tsaro ta kasa (CISA) sun yi zargin cewa matakan da Iran ke dauka na yin kutse cikin lamarin zaben yana bata kwarin gwiwa wajen yin barna ga cibiyoyin dimokaradiyyarmu” saboda Iran “tana ganin zaben na bana yana da matukar tasiri” ga manufofinta na cikin gida, a cewar hukumomin leken asiri na Amurka

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments