Iran Ta yi Tir Da Sanarwar Da Kungiyar G7 Ta Fitar Kan Maido Mata Da Takunkumi.

Ma’aikatar harkokin wajen ta Iran tayi  Allah wadai da da irin bayanan da kungiyar G7 ta yi game da shirin nukiliyarta, kuma ta bayyana shi

Ma’aikatar harkokin wajen ta Iran tayi  Allah wadai da da irin bayanan da kungiyar G7 ta yi game da shirin nukiliyarta, kuma ta bayyana shi a matsayin munafunci da kuma canza gaskiya ,

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il baghae ya fadi cewa kungiyar G7 ta amince da matakin da ya sabama doka da rashin Adalaci da Amurka da kasashen turai 3 suka dauka na sake dawo da takunkumi kwamitin tsaro na majaliar dinkin duniya kan kasar iran, matakin da ya sabama dokar kasa da kasa.

Haka zalika ya soki kungiyar ta G7 na yi gum da baki kan shirin nukiliya Isra’ila ,yace kasashen ba su da hurumin da za su iya yin lecture kan dokokin kasa da kasa , zaman lafiya da tsaro idan aka yi la’akari da halin da suke ciki na rashin gaskiya da rikon amana.

Kasashen na G7 sun yi kira ga dukkan mambobin majalisar dinkin duniya da su yi aiki da takumkumi kuma sun yi Alkawarin basu goyon bayan dari bisa dari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted