Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da matakin gwamnatin Colombia na bude ofishin jakadanci a birnin Kudus da aka mamaye, tana mai cewa wannan matakin ya saba wa Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, dokokin kasa da kasa, da kuma ‘yancin al’ummar Falasdinu na neman ‘yancin kai.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, ma’aikatar ta jaddada cewa birnin Kudus muhimmin bangare ne na yankunan Falasdinu da gwamnatin Sahayoniya ta mamaye tun 1967, kuma “dukkan gwamnatoci su guji duk wani aiki da ya kunshi amincewa da mamayar da gwamnatin Isra’ila ta yi.”
“Daidaita alaka da gwamnatin mamaya da kuma ta kare hakkin bil’adama, ya saba wa burin samun ‘yancin kai da adalci wanda ya nuna wani muhimmin bangare na tarihin gwagwarmayar mutanen wannan kasa da Latin Amurka,” in ji sanarwar.
Tehran ta kara da cewa bude wannan ofishin jakadanci a birnin Kudus da aka mamaye ya saba wa wajibcin doka ta kasa da kasa ta Colombia – wanda ya hada da girmama ‘yancin al’umma na neman ‘yancin kai – kuma yana nufin amincewa da mamayar.
Matsayin Iran ya zo ne a daidai lokacin da ministocin harkokin waje na ƙasashe 19, ciki har da Falasɗinu, Turkiyya, Saudiyya, Masar, Jordan, da Yemen, suka kuma yi Allah wadai da buɗe wannan ofishin jakadancin a cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da suka fitar.
Buɗe ofishin jakadancin Colombia a birnin Kudus da aka mamaye ya nuna cewa an sauya manufar da tsohon shugaban ƙasa Gustavo Petro ya bi, wanda ya yanke dangantakar diflomasiyya da Isra’ila a watan Mayun 2024 saboda yaƙin kisan kare dangi da gwamnatin ta yi da Gaza.