Iran Ta Yi Tir Da HKI Da Kokarin Wanke Kanta Tare Da Rabawa Addinin Musulunci Ta’addanci

Jakadan JMI na din din din a MDD Amir Saeed Iravani ya yi tir da HKI kan yadda take amfani da Kalmar “ta’addancin Addinin musulunci’

Jakadan JMI na din din din a MDD Amir Saeed Iravani ya yi tir da HKI kan yadda take amfani da Kalmar “ta’addancin Addinin musulunci’ don rabawa addinin ayyukan ta’addanci.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Iravani yana fadar haka, a taron yaki da kin addinin musulunci a kasashen yamma da kuma kasashen da suke fama da karancin sanin addinin musulunci a duniya.

Iravani ya kara da cewa, shekaru uku da suka gabata ne babban zauren MDD ya samar da kuduri mai lamba 73/254 don yaki da kin musulmi da addinin musulunci a duniya. Jakadan ya yi tir da Banyamin Natanyahu Firai ministan HKI da yawan amfani da kalmomi wadanda suke rabawa addinin musulunci ayyukan ta’addanci.

A jiya Jumma\a 14 ga watan Maris na ko wace shekara ne Majalisar ta ware a matsayin ranar yaki da kin addinin musulunci ta duniya.

Iranawani ya bayyana cewa kasashen Turai da daman a da hannu a cikin kokarin raba ayyukan ta’addanci ga addinin musulunci, tare da kafa dokokin wadanda suke bawa wasu damar wulakanta addinai da kona littafansu masu tsarki saboda cusa gaba da kiyyar addinin musulunci da musulmi ga mutanen kasashen su. Da sunan yencin fadin al-barkacin baki.

Daga karshe jakadan ya bukaci kasashen duniya su kakkafa dokoki a kasashensu wadanda zasu bukaci zaman lafiya da mabiya ko wani addini a duniya da kuma kaucewa duk wanda rikicin saboda bambancin addini da kuma nuna wariya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments