Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kira ga kwamitin sulhun MDD da ya dauki matakan da suka dace don dakatar da keta hurumin kasarta
Wakilin dindindin na Iran a Majalisar Dinkin Duniya, a cikin wata wasika da ya aike wa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da babban sakataren Majalisar ta Dinkin Duniya da kuma Shugaban babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira da a dauki tsauraran matakan da suka dace don dakatar da laifukan da yahudawan sahayoniyya suke yi na keta haddin kasa da ‘yancin kai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Wakilin na din din din na kasar Iran a wasikar da ya aike wa Majalisar Dinkin Duniya ya lissafo jerin laifukan da yahudawan sahayoniyya suka yi wajen keta hurumin kasar Iran da cikakken ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma ayyukan ta’addancin da wannan gwamnati ja’ira take yi na rashin mutunta dokokin kasa da kasa.
Wakilin dindindin na Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: A cikin wannan wasika, Iran ta bukaci da a dauki matakan da suka dace don dakatar da wadannan ayyuka da suka saba wa dokokin kasa da kasa da kuma hukunta wadanda suka aikata su.
A cikin ‘yan kwanaki da suka gabata a zaman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya sanar da cewa: A safiyar ranar Asabar 26 ga watan Oktoba ne haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar da farmaki kan Iran da makamai masu linzami da ta harba ta sama daga Tazarar kusan kilomita 100 daga kan iyakokin Iran, ta hanyar amfani da sararin samaniyar da sojojin Amurka suka ba ta a Iraki. Wadannan makamai masu linzami sun auna radar tsaron kan iyakokin Iran da dama a lardunan Ilam, Khuzestan da kuma birnin Tehran, inda jami’an tsaron Iran suka yi nasarar kakkabo mafi yawan makamai masu linzami da kuma hana yin barna. Sai dai jami’an sojin Iran hudu tare da farar hula daya sun yi shahada a yayin da suke bajintar kare kasarsu.