Iran Ta Yi Kakkausar Suka Ga Kanada Kan Ayyana Rundinar IRGC, A Matsayin Ta ‘Yan Ta’adda

Iran, ta yi tir da kakkausan lafazi da matakin gwamnatin kasar Kanada na ayyana rundinar kare juyin juya halin musulinci na kasar a matsayin kungiyar

Iran, ta yi tir da kakkausan lafazi da matakin gwamnatin kasar Kanada na ayyana rundinar kare juyin juya halin musulinci na kasar a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.

Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya danganta matakin da na kyamar na IRGC.

Nasser Kannani, ya bayyana matakin da gwamnatin Kanada ta dauka ba bisa ka’ida ba a matsayin wanda ya sabawa ka’idoji da dokokin kasa da kasa, hasali ma a cewarsa ya tsoma baki ne a cikin harkokin cikin gida na kasashe.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi ishara da cewa IRGC tare da sauran sassan sojojin kasar, tana da alhakin kiyaye tsaron kasar Iran da kan iyakokin kasar da kuma taimakawa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin dama ayyukan ta’addanci.

Ya kara da cewa matakin da kasar ta Kanada ta dauka kan rundinar ba zai yi wani tasiri ba duba da matsayi da girman da rundinar take da shi ga al’ummar Iran.

Mista Kanaani, ya kuma bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da hakkinta na mayar da martani daidai gwargwado ga wannan mataki na Kanada.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments