Iran ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijirar a Jabalia da Khan Younis na Falasdinu.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmail Baghai ya yi Allah-wadai da munanan hare-haren na Isra’ila, yana mai cewa hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa.
A yayin da yake bayyana goyon bayansa ga al’ummar Falastinu da ake zalunta, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kakkausar suka kan mummunan hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ta kai kan matsugunan ‘yan gudun hijira da kuma sansanonin ‘yan gudun hijira a Jabalia da Khan Younis, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa da dama wadanda ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da kananan yara.
M. Baghai ya bayyana cin zarafi da keta hakkin bil’adama da ka’idojin jin kai da ba a taba ganin irinsa ba a yankunan Falasdinawa da gwamnatin sahyoniyawa ta mamaye a matsayin wani babban cin zarafi ga muhimman ka’idoji da dokokin kasa da kasa.
Ya kuma yi kira da a gaggauta gudanar da shari’o’i a kan gwamnatin Sahayoniya da wakilanta da ke gaban kotun kasa da kasa (ICJ) da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) kan laifukan yaki da kisan kare dangi da cin zarafin bil’adama.