Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya yaba da sanya hannu a kan takardun yarjeniyar samar da zaman lafiya wanda kasashen Armenia da Azerbaijan suka yi. Ya kuma taya mutanen kasashen biyu murnar wannan nasara.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban Iran yana taya kasashen biyu murna a jiya lahadi, ya kuma kara da cewa, Iran a ko yauce tana fatan zaman lafiya a kasashe makobata da kasar, sabuda dalilai da dama daga ciki Iran tana amfana da kasashe makobta don kyautata yanayin tattalin arziki a tsakaninta da kasashen.
Firai ministan kasar Armenia Nikol Pashjinyan a zantawarsa ta wayar tarko da shugaban kasar Iran ya ce: Gwamnatinsa zata yi kokarin ganin an aiwatar da yarjeniyar daki-daki kamar yadda aka tsara ta.
Kasashen biyu dai sun tabka manya-manyan- yake yake a tsakaninsu, wadanda suka hada da na shekara 1992 kan yankin Nagorno Karabak, sai kuma na shekara ta 2023 inda aka kashe mutane kimani 30,000 a tsakaninsu.
A shekara ta 2023 Azerbaijan ta kwace iko da yankin Nagorno Karabak wanda a dokokin kasa da kasa yankin Azerbaijan ne, amma yan kabilar azari basu fi kashi 20% a yankin ba, a yayin da sauran kuma Armeniyawa ne. Kasashen biyu sun sami yanci ne a shekara 1991 bayan rushewar tarayyar Soviet.