Babban jami’an sojan Iran ya bada sanarwan cewa sojojin kasar ba zasu sake barin jiragen Ruwan yakin Amurka su dawo tekun farisa ba.
Tashar talabajan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Manjo Janar Ali Abdullahi yana fadar haka, Sojojin ruwa na Amurka ba za iya dawowa kusa da Iran ba, saboda Tsoron sojojin Iran. Don haka ba yanda zasu yi su sake dawowa kusa da Iran a cikin Ruwan tekun farisa.
Manjo Janar Abdullahi shi babban hafsan sojojin kasar Iran kuma babban Kwmandan sansanin sojojin kasar Mafi girma wato Khatamul Anbiya(s) ya ce sojojinsa sun rika sun gama da sojojin ruwa na kasar Amurka a yake yaken da suka gabata, kuma da yardar All..ba zasu sake komawa kusa da Iran ba.
Ya ce shugaban kasar Amurka Donal Trump da manya manyan sojojin Amurka sun sha bayyana cewa ba wanda ya kaisu karfin sojojin ruwa a duniya, da wannan kuma suke tsorata kasashen duniya.
Yace idan gaskiya ne kamar yanda Donal Trump yake riyawa, ya wargaza sojojin Iran. To me yasa sojojinsa basa matsowa zuwa mashigar ruwa ta Hurmuz. Banda haka yana riya cewa ya lalata cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran, me ya sa yake cewa ba zai bar Iran ta mallaki makaman Nukliya ba.
Ya ce a halin yanzu Shirin sojojin Iran shi ne Sanya Amurka ciki matsaloli masu yawa, a duk lokacinda suka nemi tsawaita yaki da su. Zasu kara shiga matsalolin da suka jefa kansu a ciki ne.