Babu wata ma’ana a hankalce ga damuwar da shugaban kasar Faransa ya nuna game da karfin makamai masu linzami na Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Kalaman da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi na nuna damuwa kan karfin makamai masu linzami na Iran ko kuma ayyukan nukiliyar Iran na zaman lafiya, ba ta da wata ma’ana.
Da yake amsa tambaya game da zargin shugaban Faransa a wata hira da wata jarida a yankin, Baqa’i ya ce: Damuwar shugaban Faransa game da karfin makamai masu linzami na Iran ko ayyukan nukiliyar Iran na zaman lafiya, ba ta da wata ma’ana.
Ya kara da cewa karfin makamai masu linzami na Iran an tsara shi ne bisa tsarin manufofin tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma hakkin halaltacciyar kariya daga duk wani wuce gona da iri, don haka ya zama wajibi don kare tsaron kasar Iran da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya ce maimaita fargabar rashin gaskiya game da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya daga kasar da ke da dimbin makaman kare dangi ba abu ne da za a amince da shi ba.