Ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ta gayyaci jakadan kasar Faransa dake nan Iran domin nuna masa kin amincewa da furucin ministan harkokin wajen kasarsa da ya shafi batunci ga Iran.
Muhammad Tanhaye wanda shi ne mai kula da bangaren kasashen turai a ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran, ya bukaci Karin bayani a hukumance dangane da abinda ministan harkokin wajen Faransa Jean Nuel Barrot ya fada akan Iran a yayin bikin ” Cannes” na fina-finai a da wani daga cikin fina-finan Iran ya sami kyauta.
Har ila yau, Tanhaye ya yi suka akan yadda gwamnatin ta Faransa ta yi amfani da bikin fina-finan domin yada manufofinta na siyasa.
Haka nan kuma ya ce; Faransa wacce kasa ce mai goyon bayan ‘yan sahayoniya ba ta da bakin fada akan batun da ya shafi kyawawan halaye da za ta yi Magana akan hakkin bil’adama balle ta soki wasu kasashe.
Jakadan na Faransa ya yi alkawalin mika sakon na Iran ga gwamnatinsa.