Iran Ta Karyata Jita-jitar Da Ake Yadawa Ta Yiyuwar Ganawar Reza’I Da Vance

iran ta karyata jita-jitar da ake yadawa ta yiyuwar ganawa tsakanin JD vance da kuma shugaban majalisar koli ta tsaron kasa

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi yayi watsi da karyar da ake yadawa ta yiyuwar ganawa tsakanin shugaban majalisar koli ta tsaron kasar Muhsin reza’I da kuma mataimakin shugaban kasar Amurka JD vance, tare da bayyanata a matsayin karyace zalla mara tushe balle madafa,yace babu wani shiri makamancin haka

Wannan bayani yazo ne bayan da wasu kafafen yada labarai na kasashen waje suka yi ikirarin cewa za’a gana tsakanin shugaban majalisar tsaro ta kasar iran da kuma mataimakin shugaban Amurka anan gaba, Major Janaral Rezai ya wallafa a shafinsa na X cewa babu wani shirin tattaunawa tsakaninsa da wani bangaren daga Amurka

Yace ku dena yade labaran karya game da yiyuwar tattaunawa ,ya kara da cewa yakin da aka kaddamar kan kasar iran ya rusa gwamnatin Amurka, Washington na ta faman kai kawa kamar dan caca da ya shiga cikin mawuyacin yanayi,

Daga karshe yace ku dakatar da musanta sabuwar doka daga yammacin Asiya. lokacin mika wuya yayi ga sharuddan iraniyawa guda 7 da ta gabatar da su, shi ma ministan harkokin wajen iran yace yanzu ne shugaban Amurka trump zai fahimci mummunar hanyar da yabi ta kakabawa iran takunkumi da kuma matsin lambar tattalin arziki

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted