Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar iran sun sanar da kai hari kan Naurar kariyar sojojin Amurka da jiragen sama marasa matuki a sansaninta na Ali al-salim dake kasar Kuwait da sanyin safiyar yau laraba
A cikin bayanan da ofishin hulda da jama’a na dakarun suka fitar sun ce farmakin ya tarwatsa naurar tsaron da sojojin amurka ke amfani da ita a sansanin, ana bayyana sansanin ali salim a matsayin muhimiyar cibiyar sufurin jiragen sama da kuma babbar kofa ga sojojin ke shige da fice a yammacin asiya
Hakazalika rundunar ta kara da cewa wajen kare tsaron kasar iran babu wani karfi ko wata barazana da za’a yi ko kuma wani hari,da zai tafi haka nan ba tare da mayar da martani ba, kuma ba tare da la’akari da taswirar iyakar kasa ba,
Wannan sanarwar tazo ne bayan wadda dakarun kare juyin musulunci na iran suka fitar a jiya talata cewa sun kai hari kan radar tsaro ta Amurka a sansaninta na shaikh isa dake kasar Bahrain a matsayin mayar da martani kan keta hurumin kasar iran da jiragen sama marasa matuki na Amurka ke yi .