Sojojin kasar Iran sun kai hare hare tare da amfani da makaman Drons kan sansanin sojojin Amurka na Ali Assalim da ke kasar Kuwait.
Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar sojojin kasar na fadar haka a safiyar yau Laraba, ta kuma kara da cewa, sun yi amfani da makaman drons masu karfi a hare hare.
Labarin ya kara da cewa, sansanin sojojin Amurka da ke Kuwait dai ita ce, kofar shigar da makaman Amurka zuwa cikin yammacin Asia, sannan yana da muhimmanci sosai ga Amurka saboda daga nan ne suke shirin duk wani aikin soje na hadin guiwa da sauran sansanonin sojojinsu da ke yankin.
Daga karshe sojojin Iran sun bayyana cewa a ko yaushe a shirye suke su kare kasar Iran daga makiyanta musamman Amurka daga takalar da takewa JMI a yankin.
Gwamnatin Amurka ce take shirin kokarin wucewar jiragen ruwa ta barauniyar hanya na mashigar ruwa ta Hurmuz, a cikin makonnin da suka gabata jiragen ruwa da dama ne suka kamu da wuta bayan sun yi karo da nakoyoyin ruwa a cikin tekun farisa a lokcinda suke kokarin wucewa ta mashigar.
Shugaban Amurka donal Trump ya sha fadawa duniya ikon mashigar ruwa ta Hurmuz na hannunsa. Al-hali ba haka ba.