Kamfanin Barakat, mai samar da magunguna a nan JMI ya kaddamarda sabbin magunguna har 23 wanda kamfanin ya samar a cikin gida daga ciki har da riga kafi mai suna HPV.
Kamfanin dilancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan ci gaban da kamfanin Barakat ya samu mataki ne mai girma a fagen samar da magungunan da kasar Iran take bukata a cikin gida. Kuma wannan zai bude kofar samar da magunguna ko riga kafi masu tsada da wuyan samu a duniya na cututtuka daji ko (cancer) a kasar.
Ministan kiwon lafiya na JMI Mohammad Reza Zafarqandi, a jawabinda da ya gabatar a bikin gabatar da magungunan ya ce, gamayyar kamfanonin samar da magunguna na kasar Iran wato ‘Barakat Group’ ya samar da magani wanda ake kira Gardisan, wanda yake yake magance cutar HPV ko daji, farashinsa a cikin gida rabin wanda ake shigo da shi daga waje ne.
Shugaban kamfanonin ya bayyana cewa wadannan magunguna zasu shiga kasuwa ne bayan an kammala dukkan tsare-tsare da yakamata a bi don yin hakan. Ya kuma mkara da cewa samar da wadan nan magunguna ya tserawa kasar asarar dalar Amurka $43 don shigoda su daga kasashen waje a ko wace shekara.