Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta gayyaci muqaddashin jakadan kasar Oman a kasarta
Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gayyaci babban jami’in ofishin jakadancin kasar Oman a birnin Tehran a jiya Lahadi, bayan wani rade-radin da ake yadawa cewa; Mutane biyu a kasar Oman sun mutu sakamakon shan ruwan ma’adinai da aka shigo da su daga kasar Iran.
Bayan wasu zarge-zarge marasa tushe da wasu kafafen yada labarai na kasar Oman suka wallafa na alakanta mutuwar mutane biyu a masarautar Oman da shan ruwan ma’adinan da aka shigo da su daga kasar Iran, a ranar Lahadin da ta gabata ne Abdul Rasoul Shabibi, shugaban sashen ma’aikatar kula da tekun Farisa ta ma’aikatar harkokin wajen kasar ya gayyaci mai kula da ofishin jakadancin Oman a Tehran zuwa ma’aikatar harkokin wajen kasar.
Shugaban Sashe na biyu na yankin Tekun Fasha a ma’aikatar harkokin wajen kasar ya bayyana rashin amincewar kasar Iran a hukumance kan yadda kafafen yada labarai suka rika yada munanan kalamai dangane da ruwan ma’adinan da aka shigo da su daga kasar Iran, yana mai kira da a gaggauta yin karin haske kan lamarin. Ya kara da cewa bai dace a yi amfani da wani lamari da bai da alaka da ruwan sha da ake dangantawa da wani kamfanin kasar Iran, saboda lamarin yana da alaka da sabani a tsakanin wani dangi da ake kyautata zaton an kashe mutanen ne ta hanyar Sanya musu guba a abincinsu domin ramuwar gayya, sai aka danganta lamarin a matsayin wani tushe na bata sunan wani samfurin da aka shigo da shi daga kasar Iran.