Iran Ta Gargadi Kasashen Turan Da Suka Kare HKI A Watan Da Ya Gabata Daga Hare Harenta

Shugaban rundunar Qudus ta dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran Brigadier General Esmail Qa’ani y ace kasar Iran ta ja kunnen kasashen

Shugaban rundunar Qudus ta dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran Brigadier General Esmail Qa’ani y ace kasar Iran ta ja kunnen kasashen turai guda uku, Burtaniya, Jamus da kuma Faransa saboda kawo jiragen yakinsu don kare HKI daga hare haren da maida martain da JMI ta kaiwa haramtacciyar kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Janar Qa’ani yana fadar haka a jiya laraba a nan Tehran ya kuma kara da cewa : Iran tana sane da Dukkan masu aikata laifi, kuma zasu sami sakamakon day a dace da su a lokacinda ya dace.

Janar ‘Qa’ani ya na jawabi ne a zaman makokin 40 da shahadar General Mohammad Hadi Haji Rahimi babban jami’an rundunarsa wanda yake cikin mutanen da HKI ta kasha a ranar daya ga watan Afrilun wannan shekara a karamin ofishin jakadancin Iran dake birnin Damascus na kasar Siriya

JMI ta maida martani kan HKI tare da amfani da daruruwan makamai masu linzami da kuma jirage yaki na kunan bakin wake a daren 13 ga watann Afrilu. An sanyawa hare haren maida martanin “Cika alkawali’. Hare haren sun yiwa HKI barna masu yawa. Wannan duk tare da kakkabo wasu daga cikin makaman wadanda wasu kasashen turai suka yi don kare HKI daga barnan da wadannan hare haren zasu yi.

Wasu labaran sun bayyana cewa kungiyar tsaro ta NATO ta kawo jiragen yaki kimani 240 don kare HKI daga makaman kasar Iran a lokacin. Daga ciki har da kasashen jamu, burtaniya da kuma Faransa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments