Iran Ta Damu Akan Mummunan Yanayin Da Mutanen Al-Fasha Na Sudan Suke Ciki

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Yanayin da mutanen garin al-fasha na Sudan suke ciki ya yi muni, tare da

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Yanayin da mutanen garin al-fasha na Sudan suke ciki ya yi muni, tare da yin kira da a kawo karshe killace garin da aka yi da kuma bai wa fararen hula kariya.

 Mayakan “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” dake fada da sojojin Sudan ta shimfida ikonta akan sansanin ‘yan hijira na “Zamzam’ bayan kwanaki na barkewar fada a kusa da birnin al-fasha.

Daruruwan mutane ne su ka rasa rayukansu yayin da wani adadi mai yawa na ‘yan hijirar  ya jikkata.

Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana matsayar jamhuriyar musulunci ta Iran na nuna cikakken goyon bayan Sudan a matsayin dunkulalliyar kasa.

A bisa kididdigar MDD a kalla mutane 300 aka kashe a kusa da wannan sansanin na Zamzam a fadan da aka yi a ranakun Juma’a da Asabar.

Har ila yau MDD ta kuma ce,wani adadin na mazauna  yankunan  Zamzan da Abu Shok da garin al-Fashar da sun kai 400,000 an tilasta musu ficewa daga gidajensu. Haka nan kuma wasu mutanen da sun kai miliyan 13 sun gudu, zuwa inda za su sami aminci a cikin gida da kuma wajen kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments